ANI GOMA (10) NA SHAN KURKUR TARE DA MADARA.

 ANI GOMA (10) NA SHAN KURKUR TARE DA MADARA.

.......................................................

Kurkur a turance ana kiransa da Tumeric.Ana samun shi a kasuwannu da wajajen cibiyoyin Islamic medicine.yana da amfani sosai ta 6angaren kiwon lafiya,rigafi da magance wasu daidaikun cutuka.

Za a nemi karamin cokali ayi amfani da shi,za a saka daya na garin tumeric sai a gauraya da rabin jaka ko sachet na madarar peak.za a yi haka ne a lokacin da ake da bukata da yin haka.

1.Yana kara karfin garkuwar jiki.Ta yanda jiki zai samu damar iya yaki da kwayoyin cuta da kuma baiwa jiki kariya daga barazanar kutsowar wasu abokan gaba.

2-yana magance zafin jiki da yawan gumi.

3.za a iya sha idan ana fuskantar barazanar kamuwa da ciwon daji waton cancer,sai a sha ba tare da an sanya madara ba.

3-Ana hadawa a baiwa yara su sha,dan karin karfin basira dana kokolwa.

4-za a iya sha a sanda ake neman magance rashin samun isashen bacci a jiki.

5.Magance yawan damuwa da rikirkicewar jiki.

6.ciwon jiki da kasala ga masu anemia.

6.Yawan mantuwa.

7.magance ciwon sugar amma kada a sha a tare da madara,kurkur din kawai za a sha da safe sai a zan motsa jiki har sai an yi gumi.

8-maganin kumburin wani sashe na jiki ko ga6a.

9.ciwon jiki na arthritis.

10.magance cutukkan ciki.

11.karawa fata armashi da lafiya.

12.tace wasu sinaddirran dake yiwa jiki lahani

13.rage yawan hawan jini.

14.Rage tai6a.

15.maganin ciwon kai,da jiki.u

16 caza kwakwalwa.

Ga wadanda madara ke sanyasu kornafi ko kumburin ciki ko tusa sai su zan sha a tare da kirfa kawai.

Za a sha bayan an ci abinci sau daya.

Comments

Popular posts from this blog

nin Agwaluma Ga Lafiyar Dan Adam

KARIN JINI TAKE (BLOOD)