KARIN JINI TAKE (BLOOD)

 Ganyen Ugu wanda wasu ke kira da kafi likita,ganye ne da ake samu a sassa daban daban a Nigeria,ko da yake anfi yawan samun ganyen a kudancin Nigeria inda mafi yawan Yorubawa da Igbo suka fi amfani da shi a matsayin ganyen da ake miya da shi ko ake sanyawa a turmi ayi blending a tace a sha a matsayin magani.

Ba a Nigeria kadaiba harta da wasu kasashen duniya suna amfani da ganyen ugu sabili da muhimmancin da yake da shi musamman ta 6angaren maganin cutuka da karin lafiyar jinin jikin dan adam kama daga kananin yara,mata masu juna biyu,masu fama da yawan jinya,tsofaffin da suka manyanta gami da wasu kananin rashin lafiyoyin dake addabar al'umma.

Mai ganini hajijiya ya nemi ganyen ugu ya wanke yayi blending nashi ya zuba ruwa kadan ya sanya maltina ya sha.

Ganyen ugu na kumshe da wasu ke6a66un sinadirrai masu muhimmanci ga lafiyar jiki masu taimakawa dan saurin samun warka daga ciwo a jiki da kuma karfafa guiwar sojojin yaki da kwayoyin cuta.

Yana kumshe da sinadiran dake wanke dattin ciki da na babbar hanzanya.

Yana kuma magance anemia.

Ganyen ugu na karin jini : sai a nemi ganyen a markade da blender sai a zuba a ruwa masu kyau a tace misalin cup daya sai a sanya gwango daya na maltina sai a sha,wannan hadin nada tasiri sosai ga jikin mai fama da karamcin jini a dalili da jinya ko jin ciwo ka rashin karfin jiki.

Ganyen ugu na maganin convulsion : za a yi blending na ganyen a tafasa ruwa cup daya sai a tace a ajiye idan ya huce sai a tarfa ruwan kwakwa cokali uku a sha.

Ganyen ugu na rage kitsen tumbi - sai a rinka blending din ganyen sai a tace da ruwan dumi idan sun huce sai a sha rabin cup da safe da kuma sanda za a konta.

Gyaran mamma ga mace mai shayarwa - idan uwa tana shayarwa kuma tana fuskantar karamcin ruwan nono to sai ta fake amfani da ruwan ganyen ugu da kuma maltina.

Yana gyara maniyin daya tsinke ya koma ruwa zalla.

Yana zama a matsayin natural antibiotic dake maganin mafiyawan cutukan da kwayar cuta ta bacteria ke haddasawa.

Yana wanke koda da hanta daga cuta. A sha ruwan ganyen rabin cup a kullum ba tareda maltina ba.

Ciwon suga, a tafasa sai a tace a sha cup daya tinda safe.

Dan karin karfin garkuwar jiki sai a fake shan ruwan ganyen ugu za a tarfa cokali biyu na zuma a ciki idan ya huce sai a sha.

Karin lafiya da karfin jiki shima za'a sha a tare da zuma.

Mace mai juna biyu-mata da dama suna fuskantar wasu yan rashin lafiyoyi a sanda suka samu juna biyu,wasu yawan amai,wasu tsananin kasala da ciwon jiki,wasu ciwon kai,wasu rashin iya cin abinci,da dai sauransu.To sai a rinka shan rabin cup na ganyen

ugu idan ana bukata sai a sanya rabin gwangwanin madara(peak

) ko gwangwanin Maltina daya sai a juye a ciki a gauraya da kyau a sha.za a ji dadin hadin korai da gaske.

Rashin lafiyoyin da ake tashi dasu da safe(morning sickness) sai a sha ganyen ugu rabin karamin Kofi Kamin a karya.

Ciwon hanta type A,shima a zanka shan ruwan ganyen ugu su kadai da safe.

Hawan jini da kuma rashin samun isashen bacci to sai a markade ganyen ugu a zuba ruwa masu kyau a tafasa a tace a sha muntuna talatin kamin a kwanta bacci

Mai fama da jinyar wani ciwo a jiki ya zanka shan ugu da maltina.

Mai fama da kasala da rashin karfin jiki sanadin karamcin jinin jiki ya zanka shan Ugu da Maltina.

Mai bukatar samun jini isashe har ya bayar ga wani marar lafiya ko mabukaci a asibiti to ya zanka shan ugu da maltina.

Mace da ta haihu,jini ya zuba sosai ta fake shan Ugu da maltina a kullum tsawon sati biyu.

Mai fama da zubar jini sanadin wani rauni ko ciwo a jiki ya zanka shan ganyen ugu da maltina.

Masha Allah

08063798977

Comments

Popular posts from this blog

ANI GOMA (10) NA SHAN KURKUR TARE DA MADARA.

nin Agwaluma Ga Lafiyar Dan Adam