KARIN JINI TAKE (BLOOD)
Ganyen Ugu wanda wasu ke kira da kafi likita,ganye ne da ake samu a sassa daban daban a Nigeria,ko da yake anfi yawan samun ganyen a kudancin Nigeria inda mafi yawan Yorubawa da Igbo suka fi amfani da shi a matsayin ganyen da ake miya da shi ko ake sanyawa a turmi ayi blending a tace a sha a matsayin magani. Ba a Nigeria kadaiba harta da wasu kasashen duniya suna amfani da ganyen ugu sabili da muhimmancin da yake da shi musamman ta 6angaren maganin cutuka da karin lafiyar jinin jikin dan adam kama daga kananin yara,mata masu juna biyu,masu fama da yawan jinya,tsofaffin da suka manyanta gami da wasu kananin rashin lafiyoyin dake addabar al'umma. Mai ganini hajijiya ya nemi ganyen ugu ya wanke yayi blending nashi ya zuba ruwa kadan ya sanya maltina ya sha. Ganyen ugu na kumshe da wasu ke6a66un sinadirrai masu muhimmanci ga lafiyar jiki masu taimakawa dan saurin samun warka daga ciwo a jiki da kuma karfafa guiwar sojojin yaki da kwayoyin cuta. Yana kumshe da sinadiran dake wanke datt